<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Ya Allah, Miƙa Hannunka, Ka Tsai da Haukansu LW113</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Allah, miƙa hannunka, ka tsai da haukansu,
 An kashe Almasihunka ta hannun miyagu.

[V2]
 2) Ba za ka bar Mai Tsarkinka cikin kabari ba.
 Ba za ka bar maƙiyansa su ci nasara ba.

[V3]
 3) Dā, kayayuwa tsinana sun soki goshinsa.
 Yanzu ka naɗa Almasihu a hannun damanka.

[V4]
 4) Shi wanda aka kunyata a cikin duniyan nan,
 Ka tashe shi da daraja, ka ba shi girma can.

[V5]
 5) Shi ne ya mutu dominmu, ya ɗauki giciyensa.
 Mun sami rai da lafiya ta wurin dūkansa.

[V6]
 6) Idan mun mutu tare nan, mun ɗauki giciyensa,
 Tare kuwa za mu yi murna a cikin mulkinsa.

[V7]
 7) Ina misalin yabonka, ya Yesu Almasihu?
 An sanya mulkin kome nan ƙarƙashin sawunka.</lyrics>
<hymn_number>113</hymn_number>
</song>